Kwararru Na Dari Dari Da Huldar Najeriya Da China

Buhari da Xi na China

Ganin cewa a wanan sabon shekara ta 2020, Najeriya ta ci gaba da dangantaka ta kasuwanci da Kasar sin (China), ya sa kwararru a fanin tattalin arziki da masu fashin baki a al'amuran yau da kullum na bayyana abin da su ke hange akan yadda kasar za ta amfana, ko akasin haka, a yarjejeniyoyi da ta shiga da kasar Sin ganin cewa har yanzu matasa kashi 60 cikin 100 na fama da rashin ayyukan yi a Najeriya.

Idan ba a manta ba, a ranar 12 ga watan Yuni na bara da aka yi bukin tunawa da Ranar Demokradiyya a Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba abin da zai hana Najeriya cigaba tunda kasashe irinsu China da Indiya da Indonesia su ka ci gaba. Ya ce a cikin wadannan kasashen, Indiya ce kadai ta samu cigaba a karkashin mulkin Demokradiyya.

Wadannan kalamai na Shugaba Buhari sun kara wa kasar karfin gwiwa wajen shiga wasu yarjejeniyoyi na cinikayya da musayar kudade da suka kai dallar Amurka biliyan biyu da rabi, kwatankwacin Naira biliyan 875 ko kuma Yuwan biliyan 16 a kudin kasar China.

Kwararre a harkar tattalin arzikin kasa da kasa Yusha’u Aliyu ya ce China ita ce ta ke da manya manyan ayyuka kuma ta shiga yarjejeniyoyin ne domin ta fadada karfin harkokin kasuwancinta a duniya baki daya, inda suka zuba Jari har na dallar Amurka sama da biliyan 8, ita kuma Najeriya ta shiga ne domin ta farfado da tattalin arzikinta da ke kokarin durkushewa. Kuma ya kara da cewa Najeriya ba za ta samu amfani wadanan yarjejeniyoyi kamar yadda China za ta samu ba.

Shi ma mai fashin bakin al'amuran yau da kullum Mohammed Ishaq Usman ya ce ai biri ya yi kama da mutum domin daga karshe China za ta kare ne da azabtar da kasashen ne; domin zai yi wuya a iya biyan basussukan da aka karbo a hanun ta cikin dadi.

Ga wakiliyar Sashin Hausa Madina Dauda da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Kwararru Na Dari Dari Da Huldar Najeriya Da China