Yayin da gwamnatin Najeriya ke cigaba da daukar matakan da ta ce na yaki ne da cin hanci da rashawa ne, kwararru a kasar na cigaba da bayyana abubuwan da su ke gani su ke yada al’adar cin hanci da rashawa. Wakilinmu a Abuja, Nasiru Adamu Elhikaya ya yi nuni da yadda yawan cin hanci da rashawa ya kai ga karin maganan nan cewa “marar arziki ko a mangyada aka sa shi sai ya fito a bushe” wanda akan yi amfani da shi wajen wadanda su ka ki arzuta kansu ta haram ko ta halas.
Nasiru ya ruwaito dan rajin kare dimokaradiyya Anas Dan Nayaba na cewa rashin hakuri da talauci kan sa mutane sa ‘yan siyasa tara abin duniya don maida abin da su ka kashe. Kuma talaucin kan sa mutane zaben tumun dare. Ya yi nuni da yadda yadda rashin gaskiya ya shiga bangaren ‘yansanda da sauran wurare. Y ace yawan cin hanci ya lalata al’amura sosai ta yadda wasu kamfanoni ke gudu daga Najeriya zuwa Gana.
Shi kuwa Abdulmajid Danbalki Kwamanda, daya daga cikin wadanda su ka yi yakin neman zabe ma jam’iyyar APC, ya ce ya na ganin nan gaba almundahana zai zama tarihi a Najeriya saboda Shugaba Muhammadu Buhari na yin shinfidar cimma hakan.
Your browser doesn’t support HTML5
Ga Nasiru da cikakken rahoton: