Kwararru Na Ci Gaba Da Yin Sharhi Kan Zarge-Zargen Da Ake Yi Wa Gwamnan CBN

Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele

Rundunar ‘yan sandan farin kaya ta Najeriya na binciken gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele bisa zargin aikata laifukan da suka shafi kudi, da tallafa wa ayyukan ta’addanci, da kuma yin almundahana.

Magoya bayan babban jami’in bankin, sun ce zarge-zargen da ake yi masa na da nasaba da siyasa, yayin da a gefe guda 'yan siyasa ke nuna adawa da matakin sake fasalin kudin da ya dauka.

A karshen shekarar da ta gabata ne babban bankin Najeriya ya kaddamar da sabbin takardun kudin naira don yaki da manyan laifuffuka da kuma yadda ake sayen kuri'u a lokacin zabe, lamarin da ya janyo muhawara 'yan watanni kafin zaben watan Fabrairun 2023, kamar yadda wakilin Muryar Amurka Timothy Obiezu ya ruwaito.

Laifuffukan da hukumar tsaron farin kaya ta SSS ta ke tuhumar Godwin Emefiele da su, sun hada da karkatar da akalar wani shirin bayar da bashi na biliyoyin daloli, da kuma samar da kudi don ayyukan ta’addanci.

Sabbin kudin Naira

Rundunar ‘yan sandan ba ta bayyana lokacin da ta fara binciken gwamnan babban bankin ba, amma a cewar wata sanarwar kotu, rundunar ta yi ta kokarin kiran shi domin amsa tambayoyi tun watan Disamba.

A karshen watan Disamba ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umurnin hana jami’an ‘yan sandan kama gwamnan da tsare shi ko yi masa tambayoyi, sannan ta kira binciken mara tushe balle makama.

Mai magana da yawun bankin CBN, Osita Nwanisiobi bai ce komai ba a lokacin da Muryar Amurka ta nemi jin ta bakinsa akan batun.

Emefiele dai ya fuskanci suka sosai kan manufofinsa a babban bankin kasar, ciki har da sake fasalin kudin kasar da kuma bullo da dokar kayyade yawan kudin da mutun zai cire a duk rana a watan Disamba.

Sabbin kudin Naira

Darakta a cibiyar kare hakkokin jama’a, Eze Onyekpere, ya ce Emefiele ya muzanta mukamin gwamnan babban bankin CBN ta hanyar shiga harkokin siyasa.

Emefiele dai ya janye daga neman takarar shugaban kasa a watan Mayun da ya gabata bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya umurci jami’an gwamnati da ke da muradin tsayawa takara su yi murabus.

A watan Oktoban 2022, shugaban kasar ya amince da bukatar bankin ta sake fasalin takardun kudin naira, a wani yunkuri na yaki da jabun kudade, da inganta tsarin hada-hadar kudi ta yanar gizo ko wata manhaja, da kuma rage yawan kudaden da ke yawo a kasar.

Manazarta sun ce sabbin kudin da suka sa tsofaffin kudi masu yawan gaske zama wofi, hakan zai kuma sa ya zama da wahala 'yan siyasa su sayi kuri'a a lokacin zaben watan Fabrairu.

Sai dai wani mai sharhi kan harkokin kudi, Isaac Botti, ya ce ana yiwa Emefiele rashin adalci.

kudin Najeria

“Ana yi wa mutumin bita-da-kulli, mutane na mayar da martani ne musamman a lokacin da batun sake fasalin kudi, da kayyade yawan kudin fiddawa daga banki a duk rana ya taso, wasu mutane musamman mukarraban gwamnati, matakin bai yi musu ba, suna ganin ya kamata a cire wannan mutumin, a cewar Botti.” Ya kara da cewa idan har akwai laifuffukan da ake tuhumarsa da su kan batun kudi, to ya kamata a sauke shi daga mukaminsa a kuma hukunta shi yadda ya kamata.

Sai dai Onyekpere ya ce dole ne hukumar ‘yan sandan farin kayan ta fara gabatar da kwararan hujjoji a kan ikirarinta game da gwamnan babban bankin kasar.

A watan Maris din shekarar 2014 ne dai aka nada Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya. A shekarar 2019 kuma aka sake nada shi wa’adin shekara 5 karo na 2 wanda zai kare a shekara mai zuwa.