Jam’iyyu masu goyon bayan ‘yancin kai a yankin Catalonia na kasar Spain sun lashe zaben yankin da aka gudanar da gagarumin rinjaye, abinda ya kawo cikas ga gwamnatin tarayya ta Fira-Minista Mariano Rajoy.
An shirya wannan zabe ne bayan da hukumomi a birnin Madrid suka rushe gwamnatin yankin, suka kama mafi yawancin shugabannin ‘yan awaren da suka yi kokarin ayyana ‘yancin kai bayan kada kuri’ar raba gardamar da aka gudanar a watan Oktoba, wadda aka yi cacar baki kan gudanar da ita.
Masu goyon bayan ‘yancin kan yankin Catalonia sun taru suna murnar sakamakon zaben cikin daren jiya alhamis, a lokacin da ya bayyana cewa jam’iyyu uku masu goyon bayan ballewar yankin daga Spain za su samu rinjaye da kujeru biyu a majalisar.
Amma kuma, nasarar jam’iyyu masu goyon bayan ‘yancin kan Catalonia ba ta kai mizanin da mutane da dama suka yi hankoro ba, inda suka ma rasa kujeru guda biyu daga rinjayen kujeru 4 da suke da su a baya.
Firaminista Rajoy yayi kira ga masu jefa kuri’a na Catalonia da su mayar da kwanciyar hankalin siyasa a yankin, maimakon haka, sai suka ba jam’iyyarsa ta Popular Party kashi a wannan zabe, inda ta yi asarar kujeru guda 8 daga cikin 11 da take da su a baya a majalisar yankin.
Spain da sauran kasashen Turai sun yi fatan wannan zabe zai kawo karshen rikicin siyasa a yankin, amma kuma da alamun ‘yan ra’ayin aware na Catalonia sun samu sabon karfi bisa ga wannan yanayin zaben da aka yi.