Kwanaki 285 Ke Nan Da ‘Yan Boko Haram Suka Sace Mutane a Yankin Diffar Nijar

Ministan Cikin Gida na Nijar Bazoum Muhammad

Sace mutane kimanin 39 da wasu ‘yan bindiga da aka kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne a kauyen Ngalewa dake yankin Diffa kwanaki 285 da suka gabata ya sa majalisar wakilai gayyato ministan cikin gida ya bayyanawa jama’ar kasar halin da ake ciki

Kwanaki 285 da suka wuce ne wasu ‘yan Boko Haram suka sace mata da yara kimanin 39 mazaunan Ngalewa dake yankin Diffa a Jamhuryar Nijar.

Lamarin ya faru ne a yayin wani hari da suka kai a kauyen na yankin Diffa.

Amma tun daga lokacin da abun ya faru babu wani cikakken bayani da jama’ar kasar suka samu a hukumce lamarin da ya sa majalisar dokokin kasar ta bukaci ministan cikin gida Bazoum Muhammad ya bayyana a gabansu domin jin lamarin da ake ciki akan batun.

Ministan y ace hakkin da ya rataya akansu bayan an sace mutanen shi ne su nemosu ta hanyar da ta dace ta daukan duk matakan ka kare lafiyarsu. Inji Bazoum “wannan shi ne hakkin dake kanmu saboda abun da iyalansu ke bukata shi ne su ga sun dawo gida a raye”

Da yake amsa tambaya akan abun da ya sa gwamnati bata yiwa jama’a bayani akan halin da mutanen ke ciki, sai ministan yace samun nasarar aikin abu ne da ya bukaci a yishi cikin sirri saboda haka ba zasu dinga yin surutai a kafafen yada labarai ko kuma su dinga rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta ba. Ya ce yin hakan tamkar kaskantar da kai ne.

Kafin majalisar dokoki ta bukaci ministan cikin gida ya bayyana a gabanta akan batun kungiyoyin fararen huda da ‘yan adawa sun sha sukar gwamnati suna zarginta da kasa yin wani abun a zo a gai game da lamarin. Su na zargin cewa gwamnati na nuna halin ko in-kula da abun da ya samu mata da yaran.

Kaka Tuda na wata kungiya a kwanakin baya ya shirya gangamin tayar da jama’a daga barci akan halin da mutanen da aka sace suke ciki da bukatar a cetosu. A cewarsa tunda abun ya faru basu taba jin wani dan majalisa ya sa an kira ministan cikin gida sai a wannan karon.

Souley Barman a da karin bayani