Kwamitin sulhu ya fara nazarin bukatar Palasdinawa

Wakilan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, suna ganawa.

Wani Kwamiti na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya fara nazarin bukatar Palasdinawa ta samun wakilcin Majalisar Dinkin Duniya

Jiya juma’a wani kwamiti na kwamitin sulhu na Majalisai Dinkin Duniya ya gana cikin sirri domin nazarin bukatar Palasdinawa ta neman wakilci a Majalisar Dinkin Duniya.

Yanzu haka dai kwamitin yana matakin nazari ne domin tantancewa ko bukatar ta Palasdinawa ta cika ka’idodin Majalisar da suka hadda, harda kafa gwamnatin da aka amince da ita.

A makon gobe idan Allah ya kaimu kwamitin zai sake ganawa. A ranar Laraba kwamitin sulhu ya mikawa wannan kwamiti bukatar Palasdinawan, mataki na farko a hukunce ga shirin tantancewa.

Palasdinawa suna kokarin samun amincewar Majalisar Dinkin Duniya ga bukatar su ta samun yancin cin gashi kai.

Kila za’a yi makoni kafin kwamitin ya gabatar da shawarar da ya yanke, to amma masu nazarin harkokin siyasar kasashen duniya, sunce wannan bukata da kyar tayi nasara, a saboda Amirka tayi barazanar cewa zata hau kujerar naki akan wannan bukata

Amirka dai da wasu giggan kasashen duniya suna kokarin shawo kan Palasdinawa da Isira’ila da su yiwa Allah su koma kan teburin shawarwarin samun zaman lafiya. Isira’ila tace a shirye take ta koma kan tebyurin shawarwari amma Palasdinawa sunce ba zasu koma kan teburin shawarwari ba, sai fa idan Isira’ila ta daina gina gidajen Yahudawa yan share wuri zauna a yankunan Palasdinawa.