Sojoji a Guinea Bissau sunce sun kama shugaban kasar na wucin gadi, da kuma tsohon PM kasar, gabannin zabe da za’a yi kasar dake yammacin Afirka.
Wani kakakin soja ya tabbatar da cewa suna tsare tsohon PM kuma wadda yake kan gaba a takarar shugaban kasa Carlos Gomez Jr. da shugaban wucin gadi Raimundo Preira, bayan wani hari da aka kai kan gidajensu ranar alhamis.
Leftanar kanal Daha Bana na Walna ya gayawa manema labarai jiya jumma’a cewa duka jami’an biyu suna cikin koshin lafiya.
Kwamitin sulhu na MDD yayi Allah wadai d a juyin mulki da aka yi a Guinea Bissau, kuma kwamitin yace tilas ne a sake maido da gwamnatin. Cikin sanarwa da kwamitin ya bayar yace wakilai sunyi Allah wadai da amfani da karfin soja wajen kifarda gwamnati halatacciya Guinea Bissau da wasu daga cikin rundunan sojojin kasar suka yi.
A daren Alhamis ne wasu sojojin kasar sukayi juyin mulki, washe garin ne aka ayyana fara yakin neman zabe, a zaben fidda gwani na shugabancin kasar. Sojojin suka tare hanyoyi suka kama girajen rediyo da talabijin d a ofisoshin gwamnati dake babban birnin kasar.Haka kuma sun kutsa gidajen Mr. Preira da Mr. Gomez, dan takarar da bashi da farinjini da sojoji.
Shugabannin juyin mulkin da basu bayyana kansu ba,illa wani inkiyan rundunar soja dasuka baiwa kansu,sunce basa son karbar iko a kasan. Sai dai sun dauki wan nan mataki ne domin hana wata yarjejeniya d a zata baiwa sojojin Angola damar kawowa sojojin kasar hari. Dama can sojojin kasar sunyi kaurin suna wajen katsalandan cikin harkokin kasar.