Kwamitin Sake Gina Arewa Maso Gabas Ya Kai Tallafi Adamawa Karo Na Biyu

Kayan tallafin da Kwamitin sake gina arewa maso gabas ya kai jihar Adamawa

Wannan ne dai karo na biyu da kwamitin tada komadar tattalin arzikin al’ummomin da rikicin Boko Haram ya shafa a jihohin arewa maso gabashin Najeriya,da fadar shugaban kasa ta kafa,wato Presidential Initiative For The North East,wato PINE, a takaice,ke kai irin wannan kayakin tallafin abinci ga al’ummomin da suka koma yankunansu da aka kwato na kananan hukumomin Michika da Madagali,a jihar Adamawa.

Hajiya Asma’u Joda memba ce a kwamitin,tace kwamitin zai kuma taimakawa jama’a da jari da ma bunkasa harkokin noma a yankin .

Shiko dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Michika da Madagali a majalisar wakilai Mr Adamu Kamale,yace ba su ji na- hutu ba,har sai lokacin da aka kwo karshen matsalolin da suka yiwa yankin kaka-gida.

Hon.Yusuf Muhammad shugaban karamar hukumar Madagali,yace baya ga abinci suna bukatar tsaro matuka.

Kayan tallafin da Kwamitin sake gina arewa maso gabas ya kai jihar Adamawa

Jama’an yankin dai sun nuna jin dadinsu matuka da wannan tallafi da suka samu a yanzu.

Dubban rayuka ne dai suka salwanta,baya ga wadanda aka tilastawa gudun hijira sakamakon rikicin Boko Haram da aka shafe fiye da shekaru shida ana fama,koda yake kawo yanzu hankula sun fara farfadowa a wasu yankunan.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kwamitin Sake Gina Arewa Maso Gabas Ya Kai Tallafi Adamawa Karo Na Biyu - 3' 55"