Waiwaye akan irin ayyukan da sojojin hadin gwuiwar kasashen tafkin Chadi da suka hada da Najeriya, Nijar, Kamaru, Chad da kuma Benin shi ne makasudin haduwarsu a taronsu a Jamhuriyar Nijar.
Suna nazari ne akan ainihin halin da yankin yake ciki a yau, yankin dake fama da hare-haren Boko Haram. Taron ya zo ne bayan zartas da matakan da suka shimfida a wani taron da suka yi a watanni hudun da suka gabata a kasar Chadi..
Hashimi Masa'udu ministan tsaron Nijar yace bayan taron da suka yi a babban birnin Chadi garuruwa da yawa da suke hannun 'yan Boko Haram a Najeriya duk an kwatosu. A yankin Diffa ma dake Nijar din sun yi yaki kuma yanzu ana samun sauki. Sun karkashe 'yan Boko Haram kuma yanzu basu da karfi kamar da.
Duk da nasarorin da suka samu akwai wani kalubale na daban wanda yake da alaka da nakiyoyi da 'yan ta'adan suka binne a wurare daban daban. Sanusi Imrana Abdullahi wanda injiniya ne kuma shi ne sakataren kasashen yace tabbatar da lallai 'yan Boko Haram sun binne nakiyoyi. Yanzu kokarin da su keyi shi ne na tonowa da kunce nakiyoyin.
Can baya kungiyar kasashen na yankin tafkin Chadi ta koka da rashin kudi saboda wadanda suka yi alkawarin taimakawa da kudi basu cika alkawarinsu ba. Abun da suke anfani dashi shi ne kudin da shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bayar. Cikin dala dari da shugaban Najeriya yayi alkawari ya bada tamanin da takwas shaura goma sha biyu da suke kyautata zato zai biya da zara ya samu kudi.
Kasashen duniya da suka dinga yin alkawari basu tabuka ba ba baicin taimaon da ba na kudi ba da aka ce sun ba kasashen.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5