Tambaya: Tun daga lokacin da na zama kwamandan dakarun hadin gwuiwa dake yaki da kungiyar Boko Haram wane hali ake ciki a wannan shekarar ta 2017
Amsa: Nagode da wannan tambaya. Yanzu dai ana iya cewa kungiyar Boko Haram ta gurgunta saboda kawo yanzu an karya lagontakwarai da gaske har ma ta kaiga cewa bata da wani wuri takamaimai da take da iko dashi.
Kungiyar ta tarwatse kuma sai gudu su keyi. Tana yin duk iyakar kokarinta ta rayu. Dalili ke nan hare haren da take kaiwa yanzu bai kai tsananin na da ba.
Duk hare haren da take kaiwa yanzu tana kokarin kutsa kai cikin jama’a ko ta sace dukiyarsu tare da shanu domin ‘yan kungiyar su rayu.
Tambaya:An ce wajejen ‘yan Boko Haram 57 suka rasa rayukansu a wani hari da suka yi kokarin kaiwa yaya zaka bayyana wannan lamarin
Amsa: Gaskiya ne. Yunkurin na cikin kokarinsu na cigaba da yin tasiri a yankunan da aka kwace daga hannunsu. Idan an yi la’akari da harin da suka kai sun dade suna shirin kai harin da tsammanin cewa ba’a bin sawunsu. Sun soma shirin ne a kusa da wani tsauni na Darege. Sun fara taruwa a wurin amma muna binsu a asirce. Mun shirya tsaf mu tunkaresu ta kowace hanya suka yi kokarin fitowa. Haka muka dinga binsu har sai da suka kai inda dakarunmu suke a Gaskeru. A nan aka yi ragargazasu ta yadda ya kamata ya kuma dace dasu.
Tambaya:Za’a iya cewa yankin tafkin Chadi shi ne mafakar karshe ga Boko Haram.
Amsa:Yanayin tsibiran dake kewaye da tafkin Chadi yanayi ne mai sarkakiya. Ka tuna a wurin ne ‘yan tawayen kasar Chadi da suka sha kashi suka samu mafaka. Dalili ke nan da aka kafa dakarun hadin gwuiwa na kasa da kasa. Tun wajejen 1990s ne ‘yan tawayen suka yi kakagida a kewayen tafkin.
‘Yan tsagerunsu ne suke tada karin baya a yankin. Yin la’akari da yadda wurin ke da wuyan kutsawa ciki ba za’a ce shi ne mafaka na karshe ba ga ‘yan Boko Haram. Wurin na cikin wuraren dake da wuyar kutsawa ciki a yankin. Yana da wuyar shiga da kuma wuyar samun farma ‘yan ta’adan ba tare da rutsawa da fararen hulan dake zaune wurin ba. Saboda haka muna takatsantsan wurin kai hari a yankin. Muna takatsantsan da kai hari da karfi a wurin. Dalili ke nan da za’a ga cewa harin da aka kai Gaskeru misali ne ina muka kacewa rutsawa da fararen hula.
Idan da munyi saurin kai masu hari tun farko da mun sa rayuwar wasu fararen hula cikin hadari. Sai da muka bari sun fita daga cikin jama’a kafin mu kai masu hari inda muka kakkashe kusan dukansu baicin ‘yan kalilan da suka tsira
Tambaya:Yanzu zaka ce a Boko Haram akwai banbanci tsakanin bangaren Shekau da Al-Barnawi ke nan.
Amsa:Shekau da Al-Barnawi a wurinmu, uwarsu daya. Yanzu dai akwai bangarori biyu, wato bangaren Shekau da bangaren al-Banawi amma dukansu basu da irin karfin da suke dashi da can. Sun gurgunta. Abun da suke yi yanzu kokarin karshe ne domin su nuna cewa har yanzu suna da tasiri.
Tambaya:Wasu suna kwatanta Boko Haram da macijin da aka sare amma har yanzu yana motsi yana kuma sara. Wannan kwatankwaci ne da ya dace.
Amsa:A ta nawa sai mun kama ko hallaka shugabanninsu kafin mu ce mun gama da kungiyar Boko Haram.
Tambaya:Wane irin tasiri ne taimakon kasashen waje, irinsu kasashen turai da Amurka, keyi wajen yaki da Boko Haram.
Amsa:Abu ne dake fili irin taimakon da kasashen waje ke bayarwa. Na daya idan ana batun kasashe ukun dake kan gaba wato Amurka da Birtaniya da Faransa, akwai abun da muke kira cibiyar hada duk shirye shirye wadda take Njedmina.
A nan ne kasashen nan suke taimaka mana da bayanan siri tare da yin musayar bayanan sirin kuma wannan yana aiki sosai. Suna kuma bada taimako wurin bayar da horaswa. Har ma kungiyoyin agaji da Red Cross da Red Crescent suna bada tasu irin taimakon.
Dangane da bada taimakon kudi Birtaniya tayi alakwarin pam miliyan biyar kuma ta bayar amma ta ba kungiyar kasashen Afirka ne tare da bata umurnin tayi anfani da kudin wurin taimakawa dakarun hadin gwuiwar dake fafatawa da Boko Haram.
Yawancin taimakon kudi da dakarun hadin gwuiwar ke samu yana fitowa ne daga kasashen da suka kafa dakarun. Su ne suka bada sojoji da kayan aiki da tanadin sadarwa da sufuri. Amma Najeriya ce tafi bada sojoji mafi yawa. Tayi alkawari bada taimako kuma ta cika. Kudaden da Najeriya ta bayar ne suke karfafa ayyukan dakarun.
Daga kasashen waje kungiyar hadin kan kasashen turai ta yi alkawarin bada Dalar Euro miliyan hamsin amma kamar Birtaniya ta baiwa kungiyar kasashen Afirka ne.
Ta bada umurnin a taimakawa dakarun dake fafatawa da Boko Haram da kudin wurin samar masu duk abunwan da suke bukata.
Idan ka lura duk wani bukatar dakarun daga kasashen da suka kafa kungiyar ce suke taimakawa.
Tambaya:Kuna da lokaci wani takamaimai, kaman wata uku ko hudu, da zaku ce zaku gama da Boko Haram.
Amsa:Wannan ba yaki bane na sojoji da sojoji da aka sani da suka ja daga suka fuskanci juna. Misali idan kasashe biyu na yaki ana iya harsashen lokacin da za’a kawo karshe walau a karya karfin wata kasa ko kuma a samu masu shiga tsakanin da zasu kawo sulhu. Amma wannan yakin daban yake. Kuskure ne ga kowanene yace nan da wata biyu ko shekara daya za’a kawo karshen yaki da Boko Haram. A’a. Har yanzu suna nan suna tabukawa.
Matsayin Boko Haram shekaru biyu da suka gabata ba daya yake ba da na yau. Kadan da kadan ana rage karfin Boko Haram ana karya mata lago. Za’a kuma murkusheta gaba daya nan da dan lokaci. Amma ko shakka babu a tuna fa ana yaki ne da ta’addanci wanda ba’a kawar dashi rana daya. A yi koyi da kasashen Sri Lanka da Afghanistan da Iraq da dai ire-irensu inda ake samun ayyukan ta’addanci. I,I an shawo kansu kamar kasar Sri Lanka amma daga lokaci zuwa lokaci sai a ji an kai harin ta’addanci. Saboda haka ba za’a iya cewa rana kaza za’a kawar da ta’addanci. Amma Boko Haram ta gurgunta kuma nan ba da dadewa ba zamu gama da kungiyar.