Mallam Musa Zubairu wani mai nazarin harkokin tsaro a kwalejin Kimiya da Fasaha dake Kaduna Nigeria, yace bisa bayanan da suke samu da kuma abubuwan da suke gani, kwaliya na biyan kudin sabulunta a yaki da yan Boko Haram
Yace idan aka lura hatta walwala na jama'a ta karu a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa. A saboda haka idan aka lura da wadannan abubuwa, za'a ga cewa gaskiya abubuwa kamar yadda aka yi niya ko kuma aka zata, kwaliya tana dan biyan kudin sabulun ta daidai gwargwado.
Akan cewa duk da ana samun nasara, yan Boko Haram suna ci gaba da kai hare hare, Mallam Musa Zubairu yace in ana maganar yaki da Boko Haram, ba'a yi masa kwasan karen mahaukaciya.
Yace idan aka tuna, akwai kanana hukumomi da yawa wadanda ada suke karkashin yan Boko Haram. Haka kuma ada ko daurin aure da wasu abubuwa. bai zai yiwu cikin kwanciyar hankali a jihohin arewa maso gabashin Nigeria ba.
Yanzu kuwa Alhamdullilahi ana samun saida. A saboda haka ne ya bada shawarar cewa ya kamata duk inda aka kwace, a kafa sansanin soja, domin hana yan Boko Haram komawa. A ganin su masu nazarin harkokin tsaro, kuskuren da ake yi shinr akan wuraren da aka kama, ba jami'an tsaro ko wani abu da zai nuna cewa an kama wannan wuri, ana kuma kokarin kare lafiyar mutanen da suke zaune a wadannan wurare.
Your browser doesn’t support HTML5