Kwalejin Excel a Kano ta Shirya Lacca a Kan Muhimmancin Ilimi

Jajircewa wajen neman ilimi a kowane fannin rayuwar dan Adam da kuma aiki da shi sune batutuwan da suka mamaye taron laccar da kwalejin Excel dake Kano ta shirya a jiya asabar, a wani bangare na yunkurin fadakar da Jama’a kan bukatar rungumar ilimi domin kawar da fitintunu a tsakanin al’uma.

Gurbacewar tarbiyya a tsakanin mutane musamman matasa, da gurguwar fahimtar addini da kuma jahilci kan al’amura da dama na kara yawan fititunu da kuma aikata miyagun ayyuka a cikin al’uma. Wannnan ta sanya kwalejin Excell Kano ta shirya laccar zaburar da jama’a domin daukar matakin daya dace, inji Daraktar kwalejin Hajiya Asma’u Yahya.

Taken laccar dai shine ilimi da aiki da shi ta mahangar addinin Islama. Uztaz Abdallah Musa Abdallah da ake yiwa lakabi da Penabdul shine ya gabatar da Makala a wurin taron.

Taron laccar na kwalejin Excel ya zo lokaci guda da wanda akayi Cibiyar demokaradiyya ta gidan Mambayya a nan Kano game da muhimmancin zaman lafiya da mutunta addinan juna a tsakanin al’umar arewacin najeriya, har-ma guda cikin dattawan mabiya darikar Majami’ar ECWA Reverend Mati Dangora ke cewa.

Your browser doesn’t support HTML5

KANO LECTURES