Kwale-kwale Dauke Da Kayayyakin Zabe Ya Kife, An Sace Jami’in INEC A Bayelsa

Kayayyakin Zabe jihar Bayelsa (Hoto: Facebook/INEC/Bayelsa)

A cewar Ifogah, babu wanda ya rasa ransa cikin jami’an zabe 12 da ke cikin kwale-kwalen “domin duk an ceto su tare da kwale-kwalen.”

Hukumar zabe ta INEC reshen jihar Bayesla a kudu maso kudancin Najeriya ta ce wani kwale-kwale da ke safarar kayayyakin zabe zuwa sassan jihar ya kife a wani kogi.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, jami’in yada labaran hukumar a jihar, Wilfred O. Ifogah, ya ce kwale-kwalen na kan hanyarsa ta zuwa karamar hukumar Ijawa ne a lokacin da ya yi hatsarin.

“Muna son tabbatar muku da cewa, wani kwale-kwale dauke da ma’aikata da ke kan hanyarsa ta zuwa Area-17 (Koluama) a kudancin karamar hukumar Ijaw ya kife.” Sanarwar ta ce.

A cewar Ifogah, babu wanda ya rasa ransa cikin jami’an zabe 12 da ke cikin kwale-kwalen “domin duk an ceto su tare da kwale-kwalen.”

“Sai dai mun rasa takardun rubuta sakamakon zabe, da nau’rorin cajin waya (power banks) da kayayyakin ma’aikatan.” In ji Ifogah.

Sanarwar ta kara da cewa, daukacin masu kada kuri’a da ke mazabar ta Area -17 da lamarin ya shafa su 5,368, kuma wadanda suka karbi katunan zabensu su 5,311 ne.

“Hukumar INEC na kokarin ganin ta tabbatar an yi zabe a wannan mazaba.” In ji Ifogah.

A jihar ta Bayelsan har ila yau, hukumar zaben jihar ta ce n sace jami’inta da ta tura don kula da mazaba ta Area-06 (Ossiama) a karamar hukumar Sagbama da ke jihar.

“An sace shi ne yayin da yake jira ya shiga kwale-kwalen Amassoma. Mun kuma sanar da jami’an tsaro.” Sanarwar ta ce.

A karshen makon nan za a yi zaben gwamnoni a jihohin Bayelsa, Imo da kuma Kogi a Najeriya.