Kwalara Ta Kashe Mutane Tara a Plato

Wata mata mai fama da kwalara

Ma’aikatar lafiya ta tarayya ta tura jami’an kiwon lafiya da magunguna don tallafawa masu gama da cutar kwalara a garin Namu na jihar Plato.
Ma’aikatar lafiya ta tarayya ta tura jami’an kiwon lafiya da magunguna don tallafawa masu gama da cutar kwalara a garin Namu na jihar Plato.

Mataimakin darekta mai kula da yaduwar cututuka a ma’aikatar lafiya ta tarayya Moses Anefiyan ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci marasa lafiya a garin Namu dake Karamar Hukumar Kwanfan jihar Plato.

Anefuyan yace ma’aikatar lafiya ta damu da barkewar acutar ta kwalara shi yasa ta aiko da tawaga don duba yadda lamarin yake da kuma daukar matakan gaggawa don takaita yaduwar cutar.

Anefuyan yace batun cuta kamar kwalara hakin karamar hukuma ne ta samar da tsabtatacen ruwa ga jama’arta ta kuma lura da tsabtar muhalli. Wadanda wakiliyar sashen Hausa Zainab Babaji tayi hira da su sun bayyana irin halin da suke ciki.

Shima sakataren agajin gaggawa na jihar Plato, Alhaji Alassan Barde yace sun dauki matakai domin hana yaduwar cutar. Yace ma’aikatar ruwa ta jihar Plato zata hada hannu da sauran cibiyoyi domin ganin an sami ruwan sha mai tsabta a garin Namu.

An tabbatar da mutuwar mutane tara, mutane 86 kuma suna karbar jinya a asibitoci dabam dabam na garin Namu.

Your browser doesn’t support HTML5

Rahoton barkewar kwalara a jihar Plato - 3:28