Gwamnatin jihar Borno tace kura ta natsa a garin Damboa bayan kame garin da da ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi sama da makonni ukku da suka wuce. Mataimakin gwamanan jihar Borno, Alhaji Ummar Zanna Mustapha shine ya bayyana haka a Gombe, yayinda ya ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira daga garin Damboa. Inda ya fara da gode ma gwamnaan jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dan Kunbo da al’ummar jihar baki daya akan yadda suke karbi ‘yan gudun hijarar yayinda suka shiga cikin halin kaka-nakayi.
Bayan haka mataimakin gwamnan yayi albishir din cewa, komai ya koma daidai a garin na Damboa, ‘yan gudun hijarar zasu iya komawa gidajensu. Daga karshe yayi fatan Allah ya ba jihohin zaman lafiya da kuma kasar Najeriya baki daya.
Wani dan gudun hijara da akayi hira da shi yace lallai gwamanati zata iya komar dasu amma, ba zasu iya yin kasadar kai iyalan su da sauri ba don munanan hare-haren da aka kai masu wanda ya sa suka guje ma garin, ya kara da cewa, yanzu haka akwai gawarwakin mutanen da ba su iya binnewa ba a garin. Sa’adatu Mohammed Fawu Wakiliyar muryar Amurka a Maiduguri ce ta bada wannan rahoton.
Your browser doesn’t support HTML5