WASHINGTON, DC - Kafofin yada labaran Najeriya sun ce shirin ya kunshi kusan dala miliyan 88 don sayen sabbin ‘yan majalisar. Shugabannin kungiyar sa ido a kan harkokin da suka shafi majalisun dokoki ta CISLAC da kungiyar SERAP mai sa ido kan tattalin arzikin al’umma a Najeriya, sun ce wannan kudurin tamkar nuna halin ko in kula ne ga yanayin kuncin da talakawan Najeriya ke ciki.
Kungiyar SERAP ta kuma ba hukumomin wa'adin mako guda su yi watsi da shirin.
Kungiyoyin biyu sun kira masu goyon bayan shirin marasa kishin kasa musamman a daidai lokacin da ake fuskantar tashin farashin man fetur, da hauhawar farashin abinci da sauran kayayyakin masarufi.
A wata hira da ma’aikacin Muryar Amurka Peter Clottey, Auwal Musa Rafsanjani, babban daraktan kungiyar CISLAC, ya fadi cewa ya kamata Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa ba a sayo sabbin motocin na alfarma ba don ministoci da wasu jami’an gwamnati.
Ya kara da cewa a halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, sayen wadannan motocin bai da muhimmanci a yanzu, duba da cewa ranto kudin za'a yi.
"Kamata ya yi a yi amfani da kudin don sassauta kuncin da ‘yan kasar ke ciki" a cewar Rafsanjani.