Ana tsara shirin don tallafawa ta hanyar ilimantarwa, kula da lafiya da tarbiyartarda marayun na tsawon shekara daya wanda ya soma aiki daga watan Nuwambar shekarar 2016 inji daraktan kungiyar JANNA Foundation Dr. Abdullahi Balel.
Domin gujewakada marayun su fada hannun iyaye maras adalci kungiyoyin sun yi anfani da sarakunan gargajiya, malaman addini da jami’an sashin kula da rayuwar jama’a na karamar hukumar wajen tantance iyalan da aka dankawa amanar kulawa da marayun.
Shima da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin darakta janar na Best Agenda Alhaji Ahmed Lawal ya tunatar da iyayen cewa amanar kula da marayun da suka karba Allah zai yi anfani da shi a matsayin minzanin gwajin kaifin imani da suke da shi, saboda haka ya shawarcesu su kaucewa nuna bambanci sakanin ‘ya’yan cikinsu da na riko da aka ba su.
Wasu daga cikin iyayen da wakilin Muryar Amurka ya yi hira da su Malam Mohammed Abba da Malama Jummai Mika’ilu sun bayyana mataki da kungiyoyin suka dauka da alamu ne na tausayawa tare da alkawarin anfani da bitar da suka karba wajen kula da marayun.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5