An shirya taron ne da zummar fadakar da jama'a kan mahimmancin zaman lafiya da anfanin ilimi da yaki da tsatsauran ra'ayi.
Shuaibu Muhammad shugaban kungiyar Jama'atul Walkitabu Wa Sunna ta kasar Nijar yace sun shirya taron ne domin neman zaman lafiya da fadakar da kawunan jama'a. Yace suna wayewa mutane kai game da addinin mudsulunci. Addinin musulunci baya ta'adanci, inji Muhammad. Ya cigaba da cewa duk wadanda suke zubar da jinin musulmi basu gane musulunci ba.
Yace tafiyarsu a matsayinsu na musulmai ita ce kwantar da hankulan mutane domin su gane addinin..Addinin da Annabi Muhammad (SAW) ya zo dashi na zaman lafiya ne da kare jinin mutane a karkashin addinin..Ba'a zubar da jinin musulmi sai inda ya karya dokar da addinin ya gindiya. Amma wai a je cikin masallaci a kashe musulmi ba addini ba ne. Har wanda ba musulmi ba akwai hakkin da addinin musulunci yace a bashi domin a zauna lafiya, inji Muhammad.
Babban kalubale da ake fuskanta shi ne na tsatsauran ra'ayin addini da wasu suke dashi suke kuma aiwatarwa musamman a bangaren wasu matasa.
Muhammad Sani wani limamin masallacin Kofar Nasarawa dake Kano a tarayyar Najeriya daga kungiyar IZALA cewa yayi kyan ilimi anfani dashi. Yace idan ana yin abu ba bisa sani ba to nan a ke samun matsala. Malamin dake koyas da addinin musulunci yakamata ya dora mutane akan ilimi ta yadda musulmi zai san cewa ba zai aiwatar da wani aiki ba sai bisa dalili da hujja. Masu tsatsauran ra'ayi suna addini ne akan son zuciyarsu. Yace ilimi baya koyas da zafin rai ko taurin kai ko ta'adanci.
Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5