Kungiyoyin Mata Na Kira Da A Dai-Daita Sahun Siyasa A Najeriya

A dai-dai lokacin da Jam'iyyar adawa ta PDP tace ta shirya tsaf don shigar da kara akan sakamakon zaben da aka yi, wanda Shugaba Muhammadu Buhari yayi galaba.

Batun ya tunzura gamayyar Kungiyoyin Mata wato NCWS, inda Shugabar kungiyar Madam Gloria Laraba Shoda, ta yi kira ga tsohon Mataimakin Shugaban kasa, kuma dan takarar jam'iyyar adawa ta PDP Alh. Atiku Abubakar, da yayi hakuri ya amince da sakamakon zaben.

Ba don komi ba, amma don girmama kasar da ganin girman ta, Gloria, ta ce Najeriya har yanzu tana matakin koyon tsarin Demokradiya ne, domin kuwa kasashen da suka kai shekaru 100 zuwa 200 ma har yanzu ba su kware ba koyo suke yi.

Babu zaben da za ayi ba za a samu kuskure ba, tunda mutane ne ke yin zaben, saboda haka akwai ajizanci na dan adam, dole a samu kurakurai.

Ita ma Shugabar Gamayyar Kungiyoyin Siyasa a Nahiyar Afrika Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu, cewa tayi ai gaba tafi baya nisa, saboda haka suke rokon Atiku Abubakar da ya yi hakuri ya amince da sakamakon zaben.

Ita ma 'yar siyasa daga Jihar Kaduna shugabar kungiyar Buhari Mass Movement (BMM) Hajiya Maryam Yunusa Danjaki, ta ce a zabe dole ne a samu mai ci da wanda ya fadi, kuma idan Allah ya kaddara Atiku Abubakar zai shugabanci Najeriya zai yi.

Tana mai mika roko ga Shugaba Buhari da yayi kokarin cika alkawalin da ya dauka na kyautata wa kowa, musamman mata da suka yi ruwa suka tabbatar da ya ci zaben bana.

A yanzu dai za a sa ido a ga irin tasirin da kiraye kirayen zai yi a dai-dai lokacin da kasar ke fuskantar zaben gwamnoni.

Ga rahoton Medina Dauda daga Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyin Mata Na Kira Da A Dai-Daita Sahun Siyasa A Najeriya 3'10"