Sai dai masu kamfanonin cikin gida a Najeriyar sun ce mayar da hankali wajen baiwa kamfanonin su kwangilolin gwamnati, shine matakin da zai rage radadin rayuwa cikin hanzari da mata da kuma sauran iyalai ke fuskanta a kasar.
Mace-macen aure, dawainiya da marayu, karancin fasahar sana’o’in hannu na zamani da rashin jari, kana da kalubalen ilimi da lafiyar iyalai, baya ga uwa uba mummunan tasirin kalubalen tsaro, na daga cikin manyan matsalolin dake dakushe rayuwar mata a Najeriya.
Dr Khadija Sagir Sulaiman, Malama a kwalejin ilimi ta tarayya dake Kano, ta ce matsalolin da mata da yara ke fuskanta ya kazamta a yanzu, inda za ka ga tawagar iyalai akan tituna suna barace-barace kuma wasu daga cikin su – ma ‘yan gudun hijira ne daga wasu sassa na Najeriya dake fama da tarzomar ‘yan bindiga.
Sai dai a cewar Malama Zainab Falaki Gumel, shugabar kungiyar Women Mobilization for Good Governance a jihar Jigawa, mafita ga wadannan matsalolin ita ce mata su shiga cikin harkokin zabe domin kafa gwamnati a dukkanin matakai, tana mai cewa, kungiyar su a yanzu ta dukufa sosai wajen fadakar da mata, musamman matasa a fadin jihar ta Jigawa, domin su gane muhimmancin fitowa su zabi gwamnati ta gari da zata biya bukatun su.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da masana harkokin tattalin arziki ke alakanta durkushewar kamfanonin cikin gida Najeriya da zurfin talauci a tsakanin ‘yan kasar, amma masu kamfanonin gida dake gine-gine da sauran aikace-aikace sun fayyace hanyoyin daya kamata a bi domin warware matsalar.
Alhaji Aminu Abubakar daya daga cikin Jami’an kamfanonin ‘yan kasa masu aikin gine-gine a Kano Najeriya, ya ce ya kamata gwamnatoci masu zuwa su rinka bada ayyukan kwangila ga kamfanoni na cikin gida wadanda ke samar da guraben ayyuka ga dinbin matasa kuma suke sayan kayayyakin aiki daga ‘yan kasuwa na cikin gida.
Masu kula da lamura dai na ganin akwai bukatar hada karfi-da-karfe tsakanin gwamnatoci a Najeriya da bangarori masu zaman kansu domin fitar da ‘yan kasar daga kalubalen rayuwa a fannoni daban daban.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5