Malam Habibu Mummuni magatakardan kungiyar malaman yace sun tsunduma yajin aikin ne domin matsalolin sun yi masu yawa bayan sun sha yin hakuri.
Gwamnatin bata cika alkawari ba saboda haka dole ne su fita daga bayanta. Malamai sun gaji da wulakancin da ake yi masu. Yace sun gane yanzu mutanen gwamnati ba yaran suke so ba ko kasar illa kansu. Inji Malam Mummuni zasu cigaba da yin yajin aiki har sai gwamnatin ta biya masu bukatunsu.
To saidai akwai wasu kungiyoyin malaman da basu shiga yajin aikin ba. A cewar Malam Abdulaziz magatakardar wata kungiyar suna nazarin yadda zasu fitowa gwamnatin kasar muddin bata iya shafewa malamin makarantar boko hawayensa ba.
Malam Abdulaziz yace makon da ya wuce sun je yajin aiki amma wannan makon nasu bangaren na tattara ra'ayoyin malaman ne akan abun da zasu yi idan har gwamnati bata biya masu bukatunsu ba.
A nasu bangaren iyayen dalibai na cewar irin wannan matsalar ta kan kare ne akan 'ya'yan talakawa. Malam Ahmadu daya daga cikin iyaye yace yana cikin bakin ciki da suka samu kansu a cikin wannan mawuyacin hali. Kullum indan malaman makaranta da gwamnati suka samu matsala talakawa abun ke shafa tare da 'ya'yansu saboda su mutanen gwamnati 'ya'yansu na cikin manyan makarantu na biya a cikin kasar ko a waje.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5