Kungiyoyin hada-hadar man petur a Najeriya sun janye yajin aikin da suke yanzu haka. Amma kuma har yanzu dai harkokin man ba su koma yadda suke ba da.
Abubakar Maigandi Dakin Gari, mataimakin shugaban kungiyar ‘yan kasuwar mai masu zaman kansu na kasa ya shaidawa Hassan Maina Kaina “cewa mutane zasu kara yin hakuri saboda inda ake zuwa dauko man ba kusa bane amma babu shakka za a sami saukin lamarin”.
Duk da cewa ‘yan Najeriya sun matsu akan lokacin da za a fara samun mai, malam Abubakar yace ya danganta ga lokacin da aka fara aikin man. Amma suna sa ran depot din man za su cigaba da lodi cikin hanzari. In aka yi nasarar haka lamarin ba zai dauki dogon lokaci ba.
Yajin aikin dai kusan kungiyayoyi 3 ke yin shi saboda dalilai daban-daban. Kungiyar Nato na yajin aiki akan rashin biyan kudaden da suke bin manyan ‘yan kasuwa, su kuma manyan ‘yan kasuwan suna yajin aikin ne akan kudaden da suke bin gwamnati na ainihin man da suke shigowa da shi. Bayan haka kungiyar PENGASAN wato kungiyar ma’aikatan mai ta Najeriya su kuma suna yin yajin aikin ne saboda rijiyoyin man da aka ce an saida ba bisa ka’ida ba.
Bisa ga zaman da aka yi kusan duka kungiyoyin sun aminta bayan da aka kira Shugabannan su akan zasu koma bakin aiki.
Ga rahoton Hassan Maina.
Your browser doesn’t support HTML5