Kungiyoyin Kwadagon Nigeria Za Su Fara Yajin Aiki

Taron kungiyar kwadagon Nigeria

Kungiyoyin kwadagon Nigeria za su fara yajin aikin gargadi domin gwamnati ta gaza cika masu alkawarin da ta yi dasu na karin albashi mafi kankanci daga Naira dubu 18 zuwa Naira dubu 65 wata

Kungiyoyin kwadagon Nigeria sun umurci duk ma’aikatan Najeriya su auka yajin aiki daga 12 na daren Larabar nan don matsawa gwamnati lamba ta kara mafi karancin albashin ma’aikata ya kai Naira dubu 65.

Kungiyoyin kwadagon 3 da su ka hada da NLC, da ULC da TUC sun ce wa’adin da su ka ba wa gwamnati na ya cika a Larabar nan kuma babu alamun kara mafi karancin albashin daga Naira dubu 18 zuwa dubu 65.

Jami’in kungiyar kwadago NLC Comrade Nuhu Toro ya ce yajin aikin na gargadi zai gudana ne zuwa fatar gwamnati ta cika wannan yarjejeniya, amma in ba a samu wata amsa ba daga nan za a ci gaba da yajin aikin na “sai baba ta gani”

Nuhu Toro yace majalisar kwadago ta NLC tun 19 ga wannan watan ta zauna ta tattauna maganar karin albashi kuma ta yanke shawarar shiga yajin aikin n agama gari babu gudu babu ja da baya sai abun da hali yayi. Sai dai idan gwamnati ta cika masu bukatunsu. Duk ma’aikatun kasar za su tsaya cik.

Nuhu Toro y ace sun riga sun umurci duk rassansu a jihohin kasar kuma za su dauki umurnin ba da wasa ba. Albashin naira dubu 18 da ake biya yanzu baya tare komi.

Baya ga wannan yarjejeniya da ‘yan kwadago ke neman gwamnatin Najeriya ta APC karkashin shugaba Buhari ta cika mu su, kazalika gwamnatin ta yi alkawarin kara albashin zuwa watan Disamba.

A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyin Kwadagon Nigeria Za Su Fara Yajin Aiki Daga 12 Na Daren Yau – 2’ 58”