Kungiyar Kwadago Ta Ayyana Shiga Yajin Aiki Akan Mafi Karancin Albashi Da Karin Kudin Lantarki

NLC

Shugaban Kungiyar Kwadago ta TUC, Festus Isifo ne ya ayyana shiga yajin aikin a yayin wani taron manema labarai daya gudanar tare da shugabannin kungiyar kwadago ta NLC a Abuja a yau Juma'a.

Kungiyar Kwadago ta NLC da takwararta ta TUC sun ayyana shiga yajin aikin gama gari tun daga Litinin 3 ga watan Yuni mai kamawa, sakamakon gazawar kwamiti mai kusurwa 3 wajen samun matsaya akan batun mafi karancin albashi da karin kudin lantarki.

Shugaban Kungiyar Kwadago ta TUC, Festus Usifo ne ya ayyana shiga yajin aikin a yayin wani taron manema labarai daya gudanar tare da shugabannin kungiyar kwadago ta NLC a Abuja a yau Juma'a.

A cewar Shugabanin Kwadagon, shawarar ta biyo bayan karewar wa'adin bukatar da suka gabatarwa gwamnatin tarayya tunda fari na kammala tattaunawa akan batun mafi karancin albashi kafin karshen watan Mayu.

Hadaddiyar kungiyar kwadagon ta taba ficewa daga tattaunawar tare da yin fatali da tayin gwamnatin tarayya har sau 2, wanda na baya-bayan nan ya kasance naira dubu 60, inda su kuma suka dage akan Naira dubu 497 a matsayin mafi karancin albashi.

Sakamakon lamuran dake faruwa, shugabannin kwadagon sun bijiro da dimbin matakai da suka hada da sabon mafi karancin albashi da nau'ukan hanyoyin sufuri da makamantansu domin rage radadin janye tallafin man fetur.