Kungiyoyin Kare Hakkin Fulani sun kai Kara A babban Kotun Kasa Da Kasa.

  • Ladan Ayawa

ADAMAWA: Kotu ta daure Barrister Bala Nigilari, tsohon gwamnan Adamawa

A wani taron manema labarai da kungiyoyin suka kira a babban birnin tarayyar Najeriya sunce har yanzu ana zaman dar-dar duk ko da jamiaan tsaron da aka kai Mambila a karamar hukumar Sardauna dake jihar ta Taraban

Jagorar Gan Fulani Association Alhaji Sale Bayere ya ce akwai wuraren da ba a iya kai dauki ba saboda tsaunuka dake Mambila, wani mataki a cewar kungiyoyin bai gamsar dasu ba, don haka zau dauki matakin da suke jin ya dace.

Alhaji Bayere yace abinda suka gaya wa duniya Kenan kuma suka roki gwamnatin tarayya ta dauki mataki ba tare da bata lokaci ba. Akan wannan barnar da aka yi masu, kuma suna kira gwamnatin tarayya har yanzu da tayi maza-maza ta biya diyya na wannan banar da akayi na rayuka da kuma dukiyoyi da gidajen mutane da aka kokkona da kuma dabbobin da suka bata wasu kuma suna hannun ‘yan taaddan kabilar Mambila, bayan wannan kuma yace suna kira ga kotun duniya, wato International Criminal Court Of Justice ita ma ba tare da bata lokaci ba, ta shigo cikin wannan al’amari tazo tayi bincike, ta kama wadannan mutanen da suka kira ta kama idan har gwamnatin tarayya tana ganin ba zata iya kama su ba, idan har ana ganin su sunfi karfin doka’’.

Shima mai Magana da yawun kungiyar Postoral Resolve Sale Momale yace abinda zaifi shine gwamnatin tarayya ta kafa dokar ta baci a jihar Taraban.

Ga Madina Dauda da Karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyin Kare Hakkin Fulani sun kai Kara A babban Kotun Kasa Da Kasa.2'52