Kungiyoyin sun ce yan gudun hijiran musamman wadanda suka ketara zuwa kasar Kamaru na bukatar agaji, musamman daga gwamnatin jihar.
Hadakar kungiyoyin kare hakkin bani adaman da kuma yan fafutuka da suka hada da Centre For Human and People’s Right Advocacy da Taraba Concern Citizens Forum, sun koka ne a lokacin da suka kai ziyarar gani da ido ne a yankin na Mambilla biyo bayan korafe korafen da ake samu a yanzu kuma a ganawarsu da manema labarai shugabanin kungiyoyin biyu sun yi zargin shakulatin bangaro akan wannan matsala, koda yake gwamnatin jihar na musanta wannan zargi.
Barrister. M.B Mustafa dake cikin shugabanin kungiyoyin kare hakkin bani adaman ya bayyana abin da suka bankado. Yayin da yan fafutukar ke kokawa ita kuwa gwamnatin jihar Taraban ta bakin kwamishinan yada labaran ta Anthony Danburam ya musanta zargin cewa ba’a kulawa da yan gudun hijiran da rikicin Mambila ya rutsa dasu.
To sai dai kuma yayin da wannan ma ke faruwa,suma al’ummomin yankin Wukari da Ibbi da suma suka sha fama da tashe tashen hankula a kudancin jihar sun bukaci gwamnatin kasar ne da suma a tuna da halin da suke ciki. Jihar Taraba jihace da ke da yawan kabilu wanda kuma tasha fama da tashe tashen hankula batun da masana ke kiran da akai zuciya nesa.
Your browser doesn’t support HTML5