Kungiyoyin hamayya a Senegal na kokarin hada kai su kalubalanci shugaban kasa

Wani yana kada kuri'a a zaben shugaban kasar Senegal

Wani gungun 'yan hamayya na shirin kulla kawance domin kalubalantar Abdoulaye Wade a zaben fidda gwani

Wani gungun shugabannin ‘yan adawar Senegal na taro yau Laraba, domin kulla wani kawance da zummar samun galaba kan Shugaba mai ci Abdulaye Wade, a zaben fidda gwanin da ake shirin gudanarwa a kasar.

Dan takarar Shugaban kasa Sheikh Tidiane Gadio ya gayawa Muryar Amurka cewa, manufar taron shi ne hada kan ‘yan adawa dabam-dabam da kungiyoyi masu zaman kansu su marawa bayan babban mai kalubalantar Mr. Wade baya, wanda sai kace ya zama tsohon Firai Minista Macky Sall a halin yanzu.

“Za mu tattauna da daren Laraba domin ganin ko Macky Sall na shirye ya amince da abinda na kira shi gamayyar jama’a kuma gangamin ‘yan kasa don kawar da Mr. Wade da gwamnatinsa” in ji shi.