Kungiyoyin Fararen Hula Na Son A Bayyana Sakamakon Aikin Kwamitin Gyara Lamuran Zabe

Sanata Ken Nnamani, shugaban kwamitin da gwamnatin Buhari ta kafa domin gyara lamuran zabe

A cikin watan Oktoban bara ne ministan shari'ar Najeriya Abubakar Malami ya kaddamar da kwamitin gyara lamuran zabe a madadin Shugaba Buhari wanda tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata Ken Nnamani ke jagoranta

Kwamitin nada alhakin yin nazari akan dokokin zaben Najeriya tare da nazarin sharudan zabe da kotuna daban daban suka bayar a can baya.

Kwamitin zai kuma yi nazari akan dokokin zaben kasashe daban daban na duniya kazalika an dorawa kwamitin alhakin yin nazari akan kunshin rahoton kwamitin gyaran zabe na mai shari'a Lawal Uwais wanda marigayi shugaba Umaru Yar'Addu'a ya kafa.

Mai magana da yawun kungiyoyin fararen hula Kabiru Saidu Dakata yace tun farko abun da suka so shi ne a kafa kwamiti da zai dibi aikin da kwamitin Uwais yayi. Injishi an dade ba'a kafa wani kwamitin da zai duba aikin da kwamitin Uwais yayi ba. Kwamitin Uwais ya duba harkokin zabe da harkokin mulki da harkokin dimokradiya kanta.

Tunda aka kafa kwamitin Nnamani sun zuba ido su ga abun da zai yi da kwamitin din Uwais bai yi ba. Yace wa'adin kwamitin Nnamani ya wuce amma shiru ake ji kamar an shuka dusa.

Kugiyoyin suna tunanen shin kwamitin ya kammala aikinsa ne ya mikawa shugaban kasa rahoto a asirce ko menene yake faruwa. Suna son su 'yan kwamitin su fito su yi masu bayani saboda wa'adin da aka basu ya wuce, inji Kabiru Saidu Dakata na gamayyar kungiyoyin fararen hula da na sa kai a Kano.

Amma shugaban tsangayar koyan aikin lauya a Jami'ar Bayero Dr Mamman Lawal Yusufari wanda shi ma yana cikin kwamitin Nnamani yace yana da kyau a sani basu fara aikin akan lokaci ba. Bisa ga shirye-shiryen gwamnati idan an kafa kwamiti sai ya samu wurin zama da kayan aiki da kudaden da zai bukata na yau da gobe duk sai gwamnati ta shirya abun da kuma ba zasu faru rana guda ba.

Dr Yusufari yace yanayin aikin ma da suka shigeshi sai suka ga yana da yawa. Kana ba aikin da za'a yi masa sauri ba ne. Yace gara a nemi karin lokaci domin a yi aiki mai kyau da za'a yaba dashi. Yace ko kwamitin Uwais shekara guda aka bashi amma bai iya gamawa cikin shekara gudan ba. Ya nemi karin watanni kafin ya bada rahotonsa. Yace kwamitin na gudanar da aikinsa bisa 'yancin kai.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyin Fararen Hula Na Son A Bayyana Sakamakon Aikin Kwamitin Gyara Lamuran Zabe - 3' 25"