Wadanda aka horas sun hada da fararen hula da daraktocin ma’aikatar ma’adanai, da shugabannin kamafanoni na jihohin Agadez, da Diffa da kuma Damagaran.
Maidawa Abubakar mataimakin shugaban kwamitin zartaswa na kungiyar farar hula ta ROTAB ya bayyana dalilansu na shirya horon. Suna son ‘yan kasar su san ka’idojin kasarsu akan ma’adanan da ake samu a kasarsu da kuma ka’idojin kasashen waje. A bi abun da doka ta ce shi ne mafita domin a fitarwa ‘yan kasa hakkinsu
Kungiyoyin zasu yi gwagwarmaya su tabbatar an bi doka ta yadda za’a kare hakkin kasa da al’ummarta.
Can baya dai wasu kamfanonin kasashen waje suna hakan ma’adanai ba tare da biyan diya ko haraji ba. Ire-iren wadannan abubuwan ne ake son a kawo karshensu a cewar Maidawa. Yayi misali da kamfani AREVA wanda ya ki biyan haraji duk da cewa dokar kasa ta tanadi hakan.
Hajiya Umma Abani wata ‘yar kungiyar farar hula ta ce sun karu da horon da suka samu daga ROTAB. Sun gane hakkinsu ne su san abun da aka yi da arzikin talaka da abun da aka yi masa.
Ga Tamar Abari da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5