Kungiyoyin sun bayyana wannan bukatar ne a wajen wani taron tuntuba da Cibiyar Sa-ido Kan Harkokin Majalisu (CISLAC) tare da hadin gwiwar Hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) da kuma ofishin jakadancin kasar Switzerland suka shirya.
Haka kuma mahalarta taron sun yi dubi game da matsalolin rashin samun cikakkun bayanai daga hukumomin da nauyin kula da ‘yan gudun hijira ya rataya a wuyansu, musamman idan ya shafi badakala ko kuma cin zarafi.
Mr Okeke Anya dake zama Daraktan Sha’anin Harkokin Gwamnati na Cibiyar ta CISLAC, yace rashin samar da dokoki da kuma bayanai na cikin kalubalan dake hana ruwa gudu na magance wasu matsalolin da ‘yan gudun hijira ke huskanta.
Ibrahim Abdul’aziz na dauke da karin haske kan taron:
Your browser doesn’t support HTML5