Wasu daga cikin ‘yan majalisar Dokokin jihar Kano ne ke zargin tsohon shugaban nasu da karban wasu makudan kudade domin ya dakatar da bibiyar yadda masarautar Kano ke sarrafa kudadenta da majalisar ta fara yi can baya.
Yanzu dai kungiyoyin gwagwarmaya da rashawa da tabbatar da shugabanci nagari sun fara bayyana damuwa kan yadda kwamitin ke jan kafa wajen bayyanawa duniya abun da ya gano makonni biyu bayan ya kammala aikinsa.
Shugaban kungiyar, Saidu Dakata, yace akwai bukatar kakakin majalisar na yanzu ya tabbatar an gayawa duniya abun dake kunshe cikin rahoton,
Sai dai kuma Bello Butu Butu, shugaban kwamitin binciken, yace har yanzu suna aiki kan binciken kuma da zaran sun kammala zasu mika rahotonsu wa majalisa.
Dukl da haka, akwai wasu ‘yan majalisar irinsu Baffa Babba Danagudi dake cewa kamata ya yi majalisa ta mika maganar ga hukumar EFCC ko ICPC
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5