Kungiyoyin ba da agaji sun yi mahrabin da alkawarin da gwamnatin shugaba Trump ta yi, na ba da tallafin kudi kusan Dala miliyan 640, domin taimakawa wasu kasashe hudu da matsalar karancin abinci ke addaba, suna masu cewa tun tuni lokaci ya yi da ya kamata a tallafawa wadannan kasashe, sai dai sun kuma ce akan dauki tsawon lokaci kafin irin wannan taimako ya kai ga wadanda suke matukar bukatarsa.
Shugaban na Amurka ya sanar da tallafin ne a lokacin taron kolin kasashen G20 da suka fi karfin tattalin arziki a duniya da aka yi a Hamburg dake Jamus a karshen makon da ya gabata.
Sanar da shirin tallafin har ila yau na zuwa ne makwanni da dama, bayan da Majalisar Dokokin Amurkan, ta amince da ba da tallafin ga Najeriya da Sudan ta Kudu da Somalia da kuma Yamal.
Noah Gottschalk, babban jami’i a mai ba da shawara a kungiyar Oxfam mai gudanar da ayyukan jin-kai dake Amurka, ya koka da abin da ya kwatanta a matsayin “babban jinkiri” da aka samu wajen sanar da shirin tallafin.
Ya ce “yana da muhimmanci a gane cewa, sanar da shirin ba da tallafin a taron kolin kasashen na G20, ba yana nufin an ba da tallafin ba ne.”
Da aka tambayi, Jeremy Konyndyk tsohon direktan ofishin dake samar da taimako a sakamakon bala'i na kungiyar raya kasashe masu tasowa kan abinda ke haifar da jinkirin ba da tallafin? Sai ya ce a lokuta da dama, Amurka kan yi hobbasan ganin ta ba da irin wannan tallafi.