Kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa sun baiyana bukatar a ruguza daukacin kamfanin kula da harkokin mai na kasa NNPC, kamfanin da shugaban Nigeria ya fara yiwa muhimman sauye sauye.
Wakiliyar sashen Hausa Medina Dauda ta aiko da rahoton cewa, kungiyoyin suna son a daidaita kamfanin domin a rage mata karfi ko tasirin fada a ji akan kudaden dake shiga aljihun gwamnati.
Awwal Musa Rafsanjani, shugaban kungiyar CISLAK, kungiyar dake sa ido a hulda tattalin arziki, yace ba amfani a kyale kamfanin NNPC, in dai har za'a ci gaba da cin hanci da rashawa da kuma amfani da shi a sace kudaden kasa. Rafsanjani yace in dai kamfanin ba zai gyaru ba, gara a ruguza shi.
Barister Mainasara Ibrahim manazarci kuma kwarare a farnin siyasar zamantakewar dan Adama, yace idan aka dauki matakan daya kamata, Nigeria na iya farfado da tattalin arzikinta ba tare da dogoro da kudaden da ake samu daga man fetur ba, ganin cewa kasuwarta ta fadi kasa warwas.
Haka kuma yace bai ga amfani ajiye kamfanoni ashirin karkashin NNPC ba. Yace gara a sakarwa kamfanonn kasashen waje irinsu Shell da Chevron mara, su shigo su yi aiyuka tare da gwamnati, aga ribar da Nigeria, musamman talaka zai samu.
Your browser doesn’t support HTML5