Kungiyoyi Sun Yi Kiran A Binciki Yadda Dabinon Da Sa'udiyya Ta Tura Najeriya Ya Kare A Kasuwanni

'Yan gudun hijira a Jihar Adamawa

Biyo bayan sauya akalar dabinon sadaka na miliyoyin naira da kasar Saudiya ta turo Najeriya don a rabawa yan gudun hijira a jihohin arewa maso gabas ,da ake zargin wasu jami’an Najeriya da karkatarwa yanzu haka kungiyoyi da sauran al’umman da aka turo kayan dominsu na kiran da a gudanar da bincike.

Da alamun duk da hakurin da mahukuntan Najeriya suka baiwa kasar Saudiya ,wasu kungiyoyi a Najeriya basu daddara ba,na kiran a binciki wadanda ke da hannu a badakalar bacewar wadannan dabinon.

A Kwanakin nan nema dai ofishin Jakadancin Saudiya a Najeriya ya bayyana cewa kasar ta aikowa Najeriya tulin dabino domin buda baki ga yan gudun hijira.

Kuma idan za’a ma tuna Ministar Harkokin Kasar Waje Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim tayi alkawari da fari cewa za a raba kayan ne musamman ga ‘yan gudun hijira da ke yankin Arewa maso. To sai dai yanzu haka wannan dabino na yawo a kasuwa musamman a babban birnin tarayyar kasar Abuja ana saidawa.

Sulalewar dabinon zuwa kasuwa yanzu ya jawo cece-kuce da kuma martani inda yan fafutuka da kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa ke kira da a binciki wadanda ke da hannu a wannan badakalar.

Mallam Yakubu Musa Uba dake zama shugaban kungiyar wakilan kafofin yada labarai a jihar Adamawa wanda kuma ya fito daga yankin da rikicin na Boko Haram ya shafa,yace, su sunyi mamaki da wannan abun da ya kira abun kunya.

Gwamnatin Tarayya ta bakin Ma’aikatar harkokin kasar wajen ta ba Kasar Saudiya hakuri inda tace wasu bata-gari ne suka yi gaba da dabinon bayan an kai inda ya kamata a raba su domin su samu abin duniya.

Dr Aliyu Tilde na cikin wadanda ke bin diddigin wannan batu a yanzu,ya ce kamata yayi a zurfafa bincike.

Kawo yanzu dai duk kokarin ji daga bakin jami’an gwamnatin kasar abun ya ci tura domin kowa ka tuntuba cewa yake bada shi aka yi ba,koda yake yan fafutuka na matsa lambar ayi bincike,wanda kuma lokaci ne ke iya tabbatar da shin za’a yi ko kuma a’a!?

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Kungiyoyi Sun Kira A Binciki Yadda Dabino Na Miliyoyin Nera da Saudiya Ta Aiko Ya Bace - 3' 18"