Wannan karon kungiyoyin da'awa ne na Najeriya suka yi Allah-wadai da masu wannan dabi'ar.
Kungiyoyin da'awar su 50 karkashin inuwar kungiyar hadin kan kungiyoyin da'awa sun bi wasu kasashen Musulmi na duniya wajen nuna rashin amincewa da kalaman batanci ga Annabin Rahama Tsira da Aminci su tabbata a gare shi.
Na baya bayan nan wanda ya ja hankalin Musulmi a duniya shi ma wanda ake alakanta shugaban kasar Faransa da goya ba ya a ci zarafin Annabin rahama.
Malam Muhammad Lawal Maidoki shi ne shugaban kungiyar ta hadin kan kungiyoyin da'awa a Najeriya da ya jagoranci zaman.
Kafin wannan batun na shugaban kasar Faransa a Najeriya ma a jihar Kano an samu wani mawaki wanda aka zarga da cin zarafin Annabi wanda shi ma ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin al'ummar Musulmi.
Ko a kwanannan wata jarumar fina-finan kungiyar Kannywood mai suna Rahama Sadau ta fitar da hotunan da ke nuna tsiraici a yanar gizo wadanda suka yi sanadiyar yin kalaman batanci ga Annabi.
A gefe guda kuma, gamayyar kungiyoyin ta yabawa matasan Arewacin Najeriya akan kin shiga zanga-zangar da tskwarorinsu na kudu suka gudanar ta EndSARS wadda ta yi sanadiyar hasarar rayuka da wawure kayan hukuma da na al'umma.
A makonnin baya ne mujallar kasar Faransa ta Charlie Hebdo ta sake wallafa wani hoton batanci kan Annabi Muhammad S.A.W, lamarin da ya harzuka Musulmi a duk fadin duniya.
Kasashen Musulmi da dama sun yi Allah-wadai da shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron saboda kin yin tir da lamarin.
Sai dai rahotanni da dama sun ruwaito Macron yana cewa ba shi da hurumin ya dauki wata matsaya kan abin da mujallar ta wallafa.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir Daga Sokoto:
Your browser doesn’t support HTML5