Kungiyar kwallon kafa ta Paris-saint German tayi watsi da tayin da Barcelona ta mata kan sayen dan wasanta Neymar.
Barcelona dai tace zata ba PSG fam miliyan £40 ta hada da 'yan wasanta Ivan Rakitic dan shekaru 27 da haihuwa, da kuma dan kasar Brazil Philippe Coutinho cikin cinikin Neymar mai shekaru 26.
Neymar dai ya fito fili ya shaida wa Daraktan kungiyar Paris-saint German Leonardo, cewa baya da bukatar cigaba da zama a kungiyar a wata tattaunawa da sukayi dashi na tsawon sa'o'i uku.
Tuni dama ake rade radin cewar Neymar zai koma tsohowar kungiyarsa ta Barcelona, wacce ta sayar da dan wasan ga PSG akan kudi fam dubu £200 a shekarun baya.
Kungiyar ta PSG ta bayyana cewa zata sayar da dan wasan, amman duk kungiyar da take sansa to zata biya kudin da ta kashe kan sayen dan wasan daga Barcelona, sai dai ana ganin cewar babu wata kungiya da zata iya biyan kudin dan wasan kamar yadda kungiyarsa take bukata.