Kungiyoyi Masu Zaman Kansu, Sun Shiga Siyasa Dumu-Dumu

A wannan karon baza'a bar kungiyoyi masu zaman kansu a baya ba, wajen zaben shugabanni a zabe mai zu 2019.

Babbar kungiyar makiyayan Najeriya MIYETTI ALLAH “MACBAN” ta faiyace cewa duk ‘ya’yan ta na da ‘yancin zabar wanda su ke so, amma a kungiyance shugaba Muhammadu Buhari na APC za ta zaba ko ta ke marawa baya.

Bayanin na da nasaba kai tsaye daga babban taron kungiyar a Abuja, da ta dau wannan matsayar, amma an samu shugaban kungiyar na arewa maso gabas, Mafindi Danburam na cewa shi dai a kashin kan sa Atiku Abubakar na PDP ya ke marawa baya, da korafin shugaba Buhari bai taimakawa makiyaya ba ciki har da rashin mataki ga hallaka kimanin makiyaya 800 a Mambilla.

Sakataren Miyetti Allah na kasa Baba Usman Ngelzarma, ya ce kungiyar ta gamsu da salon mulkin shugaba Buhari, don haka ta na mara ma sa baya a 2015 da a ka samu wata kungiyar makiyaya Kautal Hore ta marawa Jonathan baya, sai mu ka tsinci kan mu tamkar ba wanda ya yarda da mu, tsakanin ‘yan APC da PDP.

Don haka wannan karo matsayin mu shine mu na tare da shugaba Buhari 100% Inji Baba Ngelzarma inda ya ci gaba da maida martani ga Danburam Mafindi.

Baba Usman Ngelzarma ya kara da wasu dalilan marawa shugaba Buhari baya, da su ka hada da lamuran da ba ma na makiyaya ko kiwo kai tsaye ba.

Har dai zuwa zabe a ranar 16 ga watan Fabrairu za a ci gaba da samun kungiyoyi na marawa gwamnati ko 'yan adawa baya.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyi Masu Zaman Kansu, Sun Shiga Siyasa Dumu-Dumu 2'10"