Kungiyoyi Masu Zaman Kansu; Neman Kudi Ne Ko Taimakon Jama'a?

Tambarin Wata Kungiyar Agaji

Shin menene yasa ake kafa kungiyoyi masu zaman kansu da suke aiki a matakai daban daban a matakin kananan hukumomi ko jihohi da ma aiki tare da gwamnatin tarayya da makamantan hukumomin daga kasashen waje.

Yawancin wadannan kungiyoyin dai an san su ne da ayyukan da suka shafi al’umma ta bangaren lafiya, zamantakewa, harkokin siyasa da kuma bada agaji da sauransu. To amma wasu jama’ar na wa abin kallon hadarin kaji da cewa ana kafa su ne kawai don amfanin kan masu kungiyoyin.

​Ganin haka ne yasa Baraka Bashir daga Kano ta yi hira da Abdulrazak Sani Alkali, shugaban wata kungiyar kiyaye kamuwa da cututtukan da ka iya yaduwa. Game da cewa, shin ana kafa kungiyoyin ne don neman kudi ko kuwa taimakon jama’a. ya nuna cewa ba’a taru an zama day aba.

Sannan masu tallafawa ire-iren wadannan kungiyoyi sai sun tabbatar da aikinta sannan suke taimakawa. A karshe dai ya nuna cewa kafa kungiyoyin taimakon al’umma masu zaman kansu suna da muhimmanci wanda tuni a Kudancin Najeriya aka yiwa ‘yan Arewacinta nisa.