Kungiyoyin Farar Hula Na Niger Sun Nuna Rashin Amincewarsu da Kasasfin Kudin 2018

Shugabannin hadakar kungiyar farar hula a jamhuriyar Niger

A karon farko hadakar kungiyoyi farar hula na jamhuriyar Niger, da murya daya ta fito ta kalubali kasasfin kudin kasar na shekarar 2018 mai zuwa saboda wasu abubuwa da taek zargin kasafin ya kunsha kuma zai yiwa talakawa illa

A karon farko hadakar kungiyoyin farar hula ta fito fili a hukumance ta bayyana adawarta da kasafin kudin shekarar 2018 wanda majalisar dokokin kasar Niger din ta amince dashi duk da korafe korafen jama'a.

Tun ranar da gwamnatin ta gabatar da kasafin a gaban majalisar kasar, ya shiga shan suka daga 'yan kasar a sakamakon lura da wasu matsanantan haraji dake kunshe cikin kasafin.

Musa Cangari na hadakar kungiyar farar hula ya yi karin haske akan korafe korafensu a taron manema labarai da suka kira. Ya ce su 'yan majalisa sun so su yiwa kasafin gyaran fuska amma sai ministan kudi ya yaudaresu tare da cewa mutane 'yan tsiraru ne ke yin korafi akan kasafin. Wai gwamnati ta yi alkawarin cikawa wasu burinsu dalili ke nan 'yan majalisar suka bi ra'ayin gwamnati.

Ya ci gaba da cewa shirin asara ne zai jawowa kasa kamar irin harajin da aka yafewa kamfanonin sadarwa da masu hakan ma'adanai. Ya ce basu dace ba. A cewarsa tunda gwamnati ta dage sai ta yi abun da ta ga daman yi, tana ganin ta isa, to kungiyoyin farar hula zasu nuna wa gwamnati cewa su ne suka isa ba gwamnati ba.

Domin tilastawa gwamnatin Niger ta soke harajin dake haifar da fargaba a zukatan 'yan kasar da suke tunanen yiwuwar fadawa cikin halin kuncin rayuwa daga watan Janairun badi, ya sa 'yan gwagwarmayar suka kira jama'a su fantsama kan titunan kasar ranar 21 ga wannan watan, inji Nuhu Muhammad Arzika na kungiyar NPCR.

A ranar, cikin kowane birnin kasar, jama'a zasu fito su yi gangami tare da jerin gwano su nuna rashin amincewarsu tare da nuna yakar shirin kasafin kudin. Idan kuma gwamnati ta yi kuskuren hana gangamin mutane zasu zauna gidajensu, wato, babu zuwa aiki ke nan.

Taron kungiyoyin fararen hula akan kasafin kudin 2018

Yunkurin saka wa dukiyar gado haraji da karawa kayan masarufi haraji da sufuri da wutar lantarki da takin gargajiya na cikin abubuwan da aka bukaci gwamnati ta duba da idanun rahama amma masu rinjaye na ganin kungiyoyin na kokarin shafawa kasar kashin kaji ne.

Ga rahoton Souley Mummuni Barma da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyoyin Farar Hula a Niger Sun Nuna Rashin Amincewarsu da Kasasfin Kudin 2018 - 2' 51"