Yanzu da yake an tabbatar da kungiyoyi 16 da zasu kara a zagayen kwaf daya na gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai, ido ya koma kan yadda za gwamutsa wadannan kungiyoyin ranar litinin mai zuwa. Yadda za ayi kuwa shi ne za a zuba wadanda suka lashe kowane rukuni a kwarya guda, wadanda suka zo na biyu kuma a daya kwaryar. Sai a rika dauko daya a wannan kwarya a hada da wata kungiya daga daya kwaryar, dokar kawai it ace ba za a hada kungiyoyi biyu da suka fito daga rukuni guda ko kuma kasa guda ba.
Kungiyoyin dake cikin babbar kwarya, watau wadanda suka lashe rukunoninsu, sune Real Madrid, Atletico Madrid, FC Barcelona, Monaco, Borussia Dortmund, Bayern Munich, Chelsea, da kuma Porto.
Wadanda suke daya kwaryar kuwa sune Juventus, Basel, Bayer Leverkusen, Arsenal, Manchester City, PSG, Schalke, da kuma Shakhtar Doetsk
Wadanda suka lashe rukunonin sune zasu fara ziyartar gidan wadanda za a hada su tare a zagayen farko na kwaf dayan a ranakun 17/18 da kuma 24 da 25 na watan Fabrairu. Sannan kungiyoyin da suke kwarya ta biyun zasu ziyarci zakarun rukunonin a ranakun 10/11 da 17/18 na watan Maris.
Your browser doesn’t support HTML5