Kungiyoyi 16 Sun Sha Da Kyar A Gasar Zakarun Turai

Kungiyoyin kwallon kafa 16 sun samu hayewa zuwa zagayen gaba cikin gasar cin kofin Zakarun Turai UEFA Champions League 2019.

A ranar Laraba 11 ga watan Disambar 2019, ne aka kammala wasan rukuni na zakarun turai, inda yanzu za'a shiga matakin kifuwa daya kwala (Knockout).

Kungiyoyin da suka samu hayewa sun hada da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dake kasar Spain, Bayern Munich, daga kasar Jamus, Juventus ta Italiya, Leipzig a Jamus, Manchester City ta Ingila, kana Paris-saint German daga Faransa.

Valencia kuwa daga kasar Spain, Liverpool ta Ingila wadannan sune kungiyoyin 8 da suka zo na daya daga cikin rukunai 8.

Sai kuma kungiyoyin da suka zo na biyu a rukunin sune Borussia Dourtmund, daga Jamus sai Chelsea daga Ingila, Lyon na kasar Faransa, Napoli daga Italiya, Real Madrid ta Spain, akwai Tottenham ta Ingila, sauran sun hada da Atalanta ta Itali da Atletico Madrid daga Spain.

Dukkannin kungiyoyin guda 16 sun fito ne daga manyan lig-lig biyar daga kasashen Turai, da suka hada da Bundisliga, Laliga, Firimiya lig, Ligue 1, da kuma Seria A.

A ranar Litinin 16 ga watan Disambar 2019, za'a fidda jaddawalin wasan zagaye na 16 a Switzerland, inda zasu kara da junansu wajen neman wacce zata kai mataki na gaba.

Za kuma a buga wasan ne tun daga ranar 18,19, da kuma 25, da 26 ga watan Fabrairun 2020.