Kungiyar rajin fifita fararen fata ta Rasha (RIM, a takaice) mai hedikwata a Petersburg, na dada fadada har zuwa kasashen waje ta wajen kakkafa rassa da kuma hadaka da wasu kungiyoyi masu makamanciyar niyya irin ta ‘yan Nazi da kuma kungiyoyin Fifita fararen fata, a wani gargadin da wasu kwararru su ka yi.
RIM na da akidar tsananin kare al’adar kasa kuma ta na fafatukar maido da tsarin shugabanci mai mallaka ma gwamnati dukiyar kasa. Kungiyar ta yi kaurin suna wajen yada manufofin kyamatar ‘yan luwadi da Yahudawa a kafafenta na yanar gizo.
A watan Afirilu, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana shugabannin kungiyar guda uku: wato da Stanislav Anatolyevich Vorobyev, da Denis Valliullovich da Gariyev da kuma Nikolay Nikolayevich Trushchalov a matsayin rikakkun ‘yan ta’addan kasa da kas ana musamman. Shi ne karon farko da Amurka ta ayyana wata kungiyar Fifita farar fata a matsayin ta ‘yan ta’adda.
“RIM kungiya ce da watakila ta ke da dubban mabiya, kungiya ce da ta bada horo ga wasu mutane biyu wadanda daga bisani su ka kai harin ta’addanci a kasar Sweden,” a cewar Jason Blazakis, daraktan cibiyar nazarin ayyukan ta’addanci, da ke California.