Kungiyar Tsaro Ta NATO Ta Gudanar da Rawan Daji Mafi Girma

Wasu Sojojin NATO

Kungiyar tsaro ta NATO ta gudanar da rawar daji mafi girma a fiyeda shekaru 10,mataki da shugaban kungiyar Jens Stoltenberg, yace ya aike da sako palo-palo ga kasashensu, da kuma ma abokan gaba.

Rawar dajin wacce na tsawon mako uku da aka fara cikin watan jiya, sojoji dubu 36 ne suka shiga daga kasashe fiyeda 30 da suke cikin kungiyar da kawayenta domin gudanar da "horo mai tsanani" da aka yi da kasashen Italiya, da Spain ko Andalusiya da Portugal.

Stoltenberg yace "NATO bata neman tsokana,"amma a shirye muke mu kare dukkannin kawayenmu."

Stoltenberg yace, NATO ta gayyaci masu sa ido daga dukkan kasashe dake cikin kungiyar da kuma kungiyar tsaro ta turai,da kuma wasu kasashe dake fadin duniya, ciki harda Rasha zuwa rawar dajin.

Ahalinda ake ciki kuma, 'Yansanda a jahar California dake nan Amurka sun kama wani mutum dan shekaru 28 da haifuw kan zargin dabawa wani sojanAmurka wuka, sojan yana cikin wadanda suka tarwatsa yunkurin kai hari cikin wani jirgin kasa na kasar Faransa cikin watan Agusta.