Kungiyar Tottenham Ba Zata Sake Kasa A Gwiwaba - Mourinho

Sabon kocin kungiyar Tottenham Jose Mourinho.

Sabon kocin kungiyar kwallon kafa na Tottenham Jose Mourinho, yace yanzu kam ba zai taba yarda ya maimaita irin kura-kuran da yayi a kungiyoyin da ya rike a baya ba.

Kocin dan kasar Putugal shine wanda ya maye gurbin Mauricio Pochettino, wanda kungiyar ta sallama a ranar Talata, bayan da mahukunta kulob din suka ga cewar a bana kungiyar ta gaza yin wani kokari.

Watanni goma sha daya Mourinho yayi batare da aiki ba, tun lokacin da Manchester United ta raba gari dashi a watan Disambar 2018, sai a ranar Laraba nan ya dawo sahun masu horaswa.

Mourinho, ya bayyana kansa a matsayin mai tawali'u a farkon taron sa da manema labarai kan aikin sa da Spurs, ya ce ya kashe lokacinsa daga kwallon kafa bayan da ya raba gari da United, sai ya zamo mai nazari akan kwallon kafa (Analysis) kawai.

Sai dai bai bayyana irin kura-kuran da yace ya tabka a baya ba, ya dai jaddada cewar ba zai sake hakanba, amman yace yasan dole ne dan adam ya zamo mai kuskure, amman ba dai a maimaita wanda ya wuce ba.

Kocin wanda ya ja ragar kungiyoyi irin su Porto, a kasarsa ta haihuwa da kuma Chelsea, Real Madrid ya bar Manchester United da banbancin maki 19 tsakanita da Liverpool a gasar firimiya lig na 2018, inda ya kashe fam miliyon £400m wajen sayen 'yan wasa 11, yace duk lokacin da bai yi nasara a wasa ba baya jin dadi.

Kocin mai shekaru 56 da haihuwa ya karbi aiki da Tottenham ne a yayin da take mataki na 14 da maki 14, a teburin bana mako na 12, ya kara da cewar a wannan kakar wasan, kulob din ba zai lashe gasar Firimiya ba, amman shekara mai zuwa zai yi bakin kokarinsa domin su lashe.