Wani wakilin kungiyar Tarayyar Turai a Najeriya ya ce kawo yanzu kungiyar ta gina kananan asibitoci 46 a kasar. Wakilin ya fadi haka ne lokacinda kuma kungiyar ke mika gudummawar motocin aikin kiwon lafiya 29 da za’a rarraba su a jihohi 24 na kasar.
An dai mika wa Najeriya motocin ne a wani kauyen Guyi dake kusa da Abuja. An kiyasta kudin motocin da cewa ya kai Naira biliyan 25 ko kuma kudin Euro miliyan 63.
Tallafin na da zummar kara karfafa yaki da cutar shan inna da ma sauran cututtuka dake nakasa yara da mata masu juna biyu a kasar.
A hirarshi da Wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya, daya daga cikin jami’an dake aiwatar da aikin, Dr. Jubirilu Labbo, ya ce da cutar ta kau amma sai ta sake bulla a jihar Borno a sanadinfama da ake da rikicin Boko Haram.Da hakan bai faru ba, da tuni hukumar kiwon lafiya ta duniya ta cire Najeriya daga jerin kasashen dake fama da cutar.
Karamin ministan kiwon lafiya na Najeriya, Dr Ehinmere shi ya jagoranci taron karbar gudummawar. Daraktan rigakafin kiwon lafiya matakin farko ta Abuja Dr. Rukayya Wamako tace tuni sun tura jami’an kiwon lafiya kauyuka.
Sai dai kuma duk da tallafin, mutanen kauyen Guyi na korafin cewa an hana ‘ya’yansu makarantun zuwa a kauyukansu. Idris Adamu, wani mazaunin kauyen, yace ba motoci suke bukata ba, makarantu su ke so domin ‘ya’yansu su daina takawa da nisa kafin su samu makaranta.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Kaya da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5