Kungiyar Taliban ta sanar yau asabar cewa zata tsagaita bude wuta kan dakarun tsaron gwamnati a duk fadin Afghanistan a cikin kwanaki uku da za a yi bukukuwan salla a karshen azumin watan Ramadan.
Tsagaita wutar ta zo daidai da bada umarnin dakatar da yunkurin murkushe kungiyar Taliban na tsawon mako guda da shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani ya yi da zai fara aiki ranar goma sha biyu ga watan Yuni.
Wata sanarwar da kungiyar mayakan ta fitar tace shugaban kungiyar Taliban ya kuma umarci mayakan kada su yi tarukansu a wuraren da farin kaya suke zaune a lokacin hutun sallar domin al’ummar kasar su sami sukunin bukukuwan cikin kwanciyar hankali. Sai dai sun lashi takobin ci gaba da kai hare hare kan dakarun kasashen ketare da Amurka ke jagoranta a kasar.
Wannan ne karon farko tun shekara ta dubu biyu da goma sha biyu da kungiyar mayakan mai kaifin kishin Islama ta tsagaita wuta a Afhanistan, inda a halin yanzu take iko ko kuma hankoron kwace ikon rabin larduna dari hudu da bakwai na Afghanistan.