Kungiyar Super Falcons Na Kan Gaba A Nahiyar Afirka.

Super Falcons

Kungiyar kwallon kafar mata ta Najeriya Super Falcons sun sami karin martaba zuwa matsayi na 32 a sunayen kungiyoyin kwallon kafa na duniya da FIFA ta fitar ajerin sunayen da take tsammanin zasu tabuka a bin kirki.

Kungiyar matan dai wato Super Falcons sun baiwa kungiyar Kamaru kashi inda suka lashe 2-0 a wasan karshe da sukayi. Koch Edwin Okon yace, matan dai sun sami adadin yawan maki ko ince point har 1,633 daga watan Satumba zuwa yau kuma zasu kasance a matsayinsu na zakarun Afirka a fannin wassan kwallon kafa, kafin zuwan wasan cin kofin duniya na shekara mai zuwa da za’ayi a Canada.

Kasar Ghana ta kasance kasa ta biyu biyo bayan Najeriya a nahiyar ta Afirka, Ghana dai nada maki 1,459 kuma tana matsayi na 50 a jerin sunaye da FIFA ta fitar a baya bayan nan, amma kasar Kamaru ta koma baya inda ta koma matsayi na 52.

Indan kuma aka duba sauran kasashen duniya za’a ga cewar kasar Germany itace a gaban duk kasashen duniya da FIFA ke tsammanin zata lashe wasan cin kofin duniyar, kasa ta biyu kuwa itace Amurka, ta uku Faransa, sai kuma Japan da Sweden.