Kungiyar River Plate Ta Fasa Saida Dan Wasanta Palacios

Kungiyar kwallon kafa ta River Plate, dake kasar Argentina ta sauya shawara, kan sayar da dan wasan tsakiyarta mai suna Palacios ga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.

Tauraron dan wasan na haskawa ne a wannan shekarar, musamman a wasannin da yake buga wa kungiyarsa ta River Plate, inda ya taimaka mata taje wasan karshe na gasar cin kofin zakarun kudancin Amurka wanda aka buga a watan daya gabata.

Kokarin dan wasan ne dai yaja hankalin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, wadda taga yakamata ta dauke shi don ta rabashi da kungiyarsa, hakan dai bayyi wa kungiyarsa ta River Plate dadi ba, musamman ta yadda Real Madrid ta nemi dan wasan ta bayan gida ba batare da sanin shugabannin kungiyar ba.

Wannan dalilin yasa kungiyar tace baza ta sake zama da Real Madrid ba akan maganar dan wasan ba.

Sai dai akwai rade dadin da ke cewar anyi kusan kammala cinikin dan wasan kafin rufe hada hadar 'yan wasa a watan Janairu 2019.

Da farko dai kungiyar kwallon kafar ta River Plate ta so ta karawa dan wasan sabon kwantaraki wanda hakan zai zama mai wahala Real Madrid ta iya biyan kudinsa, amma kawo yanzu Real Madrid din ta amince za ta biya
Yuro miliyan 30 akan dan wasan mai shekaru 20 a duniya, ya zuwa yanzu abubuwa sun canza kan batun.

Dan wasan dai yayi farin jini domin manyan kungiyoyin kwallon kafa a duniya wanda suka hada da AC Millan na kasar Itali, da Chelsea da Inter Millan, sun nuna sha'awarsu kan zawarcin dan wasan.