Tsohon Mai tsaron bayan Manchester United, wanda yanzu ya ke horar da 'yan wasan Paris-Saint Germain, Laurent Blanc, ya fara zawarcin Angel Di Maria.
Kungiyar ta Paris Saint Germaine wacce ke jagorancin gasar Ligue Un a Faransa, ta bayyana sha’awarta ta daukan dan wasan na Manchester United ne a wani rahoto da shafin intanet na espnfc.com ya wallafa.
A cewar Blanc, kungiyarsa ta na da abubuwan da ta sa a gaba, kamar yadda ya bayyanawa jaridar L'Equipe, ya kuma kara da cewa idan har kungiyar na son ta bunkasa, sai ta dauko zaratan 'yan wasa wadanda su ke da wuyar samu.
A cewar Blanc, Di Maria dan wasa ne na kwarai, kuma abu ne mai wuya a garesu, domin basu kadai suka nuna suna son dan wasan ba, idan aka yi la'akkari da irin kudaden da kungiyoyin wasa na Ingila ke zubawa, wanda hakan ke jan hankulan 'yan wasa da dama.
Ya kuma ce kada a manta, Manchester United ta zuba makudan kudaden wajen sayen dan wasan, saboda a cewar Blanc, idan har suna son cimma burinmu, sai sun nema mafita.
Ana dai hasashen Di Maria zai kai Pam miliyan 45, idan har PSG na bukatarsa, wanda hakan kudi ne da ya gaza wanda Mancheter United ta biya da Pam miliyan 15 a lokacin da ta sayo shi daga Real Madrid.