Mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Newcastle dake Ingila, Mike Ashley, ya bayyana cewar a karshen watan Disambar da muke ciki 2018 zai saida
kungiyar.
Attajirin Ashley ya yanke wannan shawarar saida kungiyar tasa Newcastle United ne bayan ya shafe sama da shekaru 10 da sayen kulob din, Inda a tsawon lokacin da ya shafe yana rike da kungiyar, Newcastle ta fuskanci koma baya na zuwa kasa da matakin gasar Firimiya lig na Ingila har sau biyu.
Tun a shekarar 2007 Mike Ashley, ya mallaki kungiyar ta Newcastle kan zunzurutun kudi har fam miliyan £134 da kusan rabi kudin Ingila.
Ashley, yayi yunkurin saida kungiyar a shekarar 2017 ga wata attajira mai suna Amanda Staveley, amma daga bisani ya fasa sayarwa bayan ta masa tayin biyan fam miliyan dari uku.
Newcastle dai a halin yanzu tana matsayin na 15 ne a teburin gasar Firimiya lig na Ingila 2018, a karkashin horarwar Rafael Benitez a wasannin mako na sha biyar. A yau Laraba kungiyar zata fafata da Everton a wasan tsakiyar mako.